Shugabannin ɗaliban Najeriya sun mutu

Image caption Hatsarin mota yana haddasa asarar rayuka a Najeriya

A Najeriya, wasu shugabannin ƙungiyar ɗalibai ta kasar wato NANS su biyar sun rasa rayukansu yau, a sanadin wani mummunan haɗarin mota da ya rutsa da su, a kan hanyarsu ta zuwa jihar Akwa Ibom.

Yanzu haka dai ragowar shugabannin kungiyar ɗaliban da suka tsira da munanan raunuka suna kwance a asibiti ana jiyyar su.

Hadarin mota dai wata babbar matsala ce da ke haddasa asarar rayukan jama'a da dama a Najeriya.