'Mutane dubu 93 sun mutu a Syria'

Image caption Makabarta a Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane akalla dubu casa'in da uku ne aka kashe a Syria tun somin tashin hankali a can.

Alkaluman sun zarta kiyasin da aka bayar na karshe a cikin watan Janairu da dubu 30, inda mutane akalla dubu biyar suke mutuwa a kowane wata a Syria.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi amannar cewar ainihin alkaluman sun fi haka saboda mutane da yawa ne ke mutuwa ba tare da bayar da rahoto ba, kamar dai yadda Kwamishinar kula da kare hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya, Navi Pillay ta bayyana.

Alkaluman sun nuna cewar fiye da kashi 80 cikin dari na wadanda suka mutu maza ne, to amma fiye da dubu daya da dari bakwai yara 'yan kasa da shekaru 10 ma sun mutu.

Karin bayani