Amurka: Hukumar NSA za ta yi bayani

Janar Keith Alexander
Image caption Shugaban hukumar NSA, Janar Keith Alexander, ya ce zai so Amurkawa su san abin da ya faru

Sakamakon bankada sirrin shirin nan na Amurka na tatsar bayanan jama’a da jaridun Guardian da Washington Post suka yi a makon jiya, shugaban hukumar tsaron kasa ta Amurkar, NSA, ya ce zai so Amurkawa su san irin ayyukan da hukumarsa ke gudanarwa.

Janar Keith Alexander ya ce yana ganin kwarmata bayanan da Edward Snowden ya yi ya haifar da mummunar illa.

Ya kuma ce ya yi amanna Amurka da kawayenta ba su da kwanciyar hankali a yanzu kamar yadda suke da shi makwanni biyu da suka wuce.

Sai dai kuma Janar Alexander ya kara da cewa abu ne mai muhimmanci a gabatarwa al'ummar Amurka bayanan hakikanin yadda al'amarin yake daidai gwargwado.

Tuni dai ya yi magana a kan kulle-kullen kai hare-haren ta’addanci har kusan 12 a gida da wajen kasar ta Amurka, wadanda ya ce an dakile su ta hanyar amfani da bayanan da aka bankada.

Ya yi alkawarin bayyana wadannan kulle-kulle yayin wani zama na sirri da ’yan Majalisar Dattawan kasar ta Amurka za su yi ranar Alhamis.

Shugabar kwamitin da ke sa ido a kan al’amuran leken asiri a Majalisar Dattawan, Dianne Feinstein, ta ce hukumar ta NSA ta tattara bayanan wayar mutane ne kawai saboda tana tunanin wadanda aka tattara bayan nasu suna da alaka da Alkaida da Iran.

Karin bayani