A350: Jirgin da Airbus ba ya son kerawa

jirgin airbus a350xwb
Image caption Kamfanin airbus ya yi ta jan kafa wajen sanya biliyoyin daloli dan kera shi.

Bayan shafe shekaru a teburin zane-zane, da zuba jarin dala biliyan sha biyar, kamfanin Airbus ya kaddamar da sabon jirgin sa wanda ya yi tashin farko a ranar Juma'a.

Jirgin samfurin A350XWB mai fadi, kamfanin na Airbus ya ce zai kafa wani sabon tarihi a yawan man da yake amfani da shi da kuma rashin gurbata muhalli.

Hakanan babban jirgin mai dauke da injina biyu zai kasance kishiyar jirgin kamfanin Boeing mai 787 Dreamliner wanda yake ikirarin ya samar da da sabuwar fasahar zamani a kere-keren jiragen sama.

Duk da haka kamfanin Airbus bai so ya kera jirgin na A350 ba.

A tsakiyar shekaru goman da suka gabata, kamfanin kere-kere mallakar nahiyar turai yana kokarin kaddamar da jirginsa mai cin dogon zango na A380 Superjumbo.

Jirgin superjumbo mai bene, ya kasance wata na'ura mai cike da sakarkakiya, kuma kudin da aka kera shi da shi ya dinga hauhawa don haka kamfanin Airbus ya yi ta jan kafa wajen sanya wasu biliyoyin kudi don kera wani irinsa.

Sai dai Airbus na bukatar wani sabon jirgin da zai kalubalanci kamfanin Boeing da ya kera Dreamliner, wanda a yanzu haka yake jan hankalin kamfanonin jiragen sama.

Karin bayani