Amurka zata ba 'yan tawaye a Syria kayan yaki

Syria crises
Image caption Wani dan tawaye a Syria

Amurka ta ce zata bada gudunmawar kayan yaki kai tsaye ga 'yan tawayen Syria a karon farko.

Shawarar hakan ta biyo bayan sanarwar da fadar White House ta fitar ne cewa a yanzu tana da shaidu kwarara cewar sojojin gwammati sun yi amfani da makamai masu guba wajen kai hare hare, lamarin da Shugaba Obama ke cewa ya kai matsayin da ba zasu iya zuba ido ba.

Ita dai Rasha wadda ke goyon bayan gwamnati Syria na cewa hujjojin da Amurka ke cewa tana da su, ba masu gamsarwa ba ne.

Cibiyoyin leken asirin Amurka sun tabbatar da cewa gwamnatin Syria ta yi amfani da makamai masu guba kuma hakan ya tsallake jan layin da shugaba Barack Obama ya shata da kansa.

A yanzu shugaba Obama yana da aniyar taimakawa 'yan tawayen Syria ta hanyar amfani da karfin soji.

Ina hujja?

Sai dai duk da cewa Amurkan ta dau wannan mataki kawo yanzu gwamnatin Shugaba Obama na taka tsan-tsan kan yadda za a shawo kan rikicin Syria saboda kawo yanzu akwai rarrabuwar kawuna game da matakin da za a dauka da kuma abun da ka iya biyo baya.

Kodayake manufofin Amurka na sauyawa, sai dai kawo yanzu babu cikakken bayani game da irin matakin da Amurka ke son ta dauka.

Misali ko za'a yi amfani da ra'ayoyin jama'a a matsayin wata hujja da ta sa Amurkan ta sauya manufofinta?

A watan Afrilun da ya gabata, an ce cibiyoyin leken asirin Amurka sun samu karfin gwiwar cewa gwamnatin Syria na amfani da makamai masu guba.

Sai dai hukumomi a Faransa da kuma Birtaniya sun fi fitowa fili wajen karfafa maganar.

A yanzu nazarin da Amurka ke yi, ya kusan zuwa iri daya da nasu.

A cewar wani mai ba shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Benjamin Rhodes "suna da tabaccin cewa dakarun gwamnatin Syria sun yi amfani da makamai masu guba da suka hada da sinadarin Sarin akan 'yan adawa a lokuta da dama a bara."

Shin ko menene ya sauya?

Shin an samu kwararan shaidu?

Haka kuma ko za'a iya shawo kan jama'a game da lamarin?

Taka tsan-tsan

Babbar tambayar a nan ita ce ko wanne irin mataki ne Amurka za ta dauka?

Tun farko Amurkan ta nuna kamar za ta taimakawa 'yan tawaye da kananan makamai.

Mr Rhodes ya kuma ce shugaba Obama bai yanke shawarar amfani da karfin soji ba ko haramta zirga-zirgar jiragen sama da kuma tura sojojin kasa zuwa Syria.

Ko da yake taka tsan-tsan da shugaban Obama ke yi abu ne da ya dace, amma masu kamun kafa a Amurka sun jadada cewa ya kamata ya kara zage dantse.

Akwai manyan kalubale saboda Syria na tsakiyar da dama daga cikin matsalolin da yankin ke fuskanta.

Bazuwar rikicin zuwa wasu wurare ka iya hadasa yaki a yankin abun da kan iya janyo Lebanon da kuma watakila Israila.

Haka kuma rikicin mai yiwuwa ya shafi Iraki da watakila Jordan.

Bukatar da 'yan adawa suka shigar akan a taimaka masu da makaman harbo tankunan yaki da jiragen sama mun fahimci cewa batu ne da kawo yanzu ake kan tattaunawa a kai.

Taron G8

Ra'ayin Amurka da Faransa da Birtaniya shine cewa a ba batun hada gwamnatin Syria da ' yan adawa kan teburin sulhu a birnin Geneva fifiko.

Sai dai ko matakin da Amurkan ta dauka ya janyo lauje a cikin nadi a kokarin samar da taron zaman lafiya?

Shin ko wanne irin mataki Rasha zata dauka?

Wadanan zasu kasance abubuwan da zasu ja hankalin mahalata taron kasashen duniya masu karfin tattalin arziki watau G8 da za'a yi a makon gobe a yankin Arewacin Ireland.