Masu zabe sun fara kada kuri'a a Iran

Masu kada kuri'a a Iran
Image caption An fara kada kuri'a don zaben wanda zai maye gurbin Shugaba Ahmadinejad a Iran

An fara kada kuri'a a Iran don zaben wanda zai maye gurbin Shugaba Mahmud Ahmadinejad.

Zaben dai ka iya yin zafi fiye da yadda aka zata a baya.

A makon da ya gabata an ga wani sauyi mai ban-mamaki a abin da alamu suka nuna zai zama zaben da kowa ya san yadda zai kaya.

Mutane shida ne kawai sunayensu suka samu shiga jerin ’yan takara bayan a watan jiya hukumomin kasar ta Iran sun haramtawa ’yan takara kusan dari bakwai tasayawa.

Kuma kusan dukkan mutanen shida magoya bayan Shugaban Addini na kasar ne, wato Ayatollah Ali Khamenei.

Sai dai dan takara daya, Hassan Rowhani, ya ci gaba da daukar hankali.

Ya fito bainar jama’a ya bayyana cewa akwai bukatar shimfida fuska ga kasashen Yamma, kuma takunkumin da aka kakabawa Iran sanadiyyar shirinta na nukiliya ya yi mummunar illa ga tattalin arzikin kasar.

Wannan, da ma kiran da Mista Rowhani ya yi da a baiwa kafofin yada labarai ’yanci, sun jawo masa goyon baya daga masu ra’ayin kawo sauyi da ma wadansu mutanen da ke adawa da hukumomin kasar.

Kuri'un jin ra’ayin jama’ar da aka gudanar dai sun nuna cewa ko dai yana kan gaba, ko kuma ba tazara sosai tsakaninsa da masu ra’ayin mazan jiyan da ke kan gaba.

Karin bayani