An fara tattaunawa da 'yan Boko Haram

Imam Abubakar Shekau
Image caption Gwamnatin Najeriya ta yi alkawarin tukwici ga wanda ya taimaka aka kama Imam Abubakar Shekau

A Najeriya, kwamitin da Gwamnatin Tarayya ta kafa don nemo hanyar sasantawa da ’yan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah lid Da’awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram, ya fara tattaunawa da mutane 104 wadanda ake zargin ’yan kungiyar ne.

Kwamitin ya gana da mutanen ne a Legas, inda ake tsare da su a gidajen yari, da nufin fahimtar juna da kuma shata matakin da za a dauka na gaba.

Ministan Ayyuka na Musamman na Najeriyar, kuma shugaban Kwamitin Sasantawar, Alhaji Kabiru Tanimu Turaki, shi ne ya jagoranci ’yan kwamitin.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ambato shi yana cewa: “Mun yi musayar ra’ayoyi da su kuma sun amsa mana tsakani da Allah; ina ganin zan iya cewa mun fahimci galibin abubuwan da suke muradi”.

Kwanan nan ne dai gwamnatin Najeriyar ta haramta kungiyar ta Boko Haram tana ayyanata a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Karin bayani