Rasha ta karyata Amurka a kan batun Syria

Image caption Shugaban Rasha, Vladmir Putin

Rasha ta bayyana babban shakku game da shedar Amurka ta cewar gwamnatin Syria ta yi amfani da makamai masu guba, abinda fadar Shugaban Amurkar ta White House ta ce ya sa za ta bayar da taimakon makamai kai tsaye ga yantawaye.

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce ta damu matuka game da shawarar, kuma samar da makaman ga yan adawa zai zafafa girman tashin hankalin.

Shugaban babbar kungiyar 'yan tawayen Salim Idris ya shedawa BBC cewar wannan wani muhimmin mataki ne, to amma ya bukaci da a gaggauta samar da makaman kakkabo jiragen sama da kuma masu dargaza tankokin yaki.

Karin bayani