Zaɓen Iran: Hassan Rouhani ke kan gaba

Image caption Hassan Rouhani, ɗan takarar zaɓen shugaban kasar Iran

Sakamako na baya-bayan nan na zaƙen shugaban ƙasar Iran na nuna cewa, mai matsakaicin ra'ayin riƙau, Hassan Rouhani ne yake ci gaba da kasancewa a kan gaba, kuma wannan ka iya ba shi damar lashe zaɓen.

Alƙaluman da hukumomi suka fitar na nuna cewa, Hassan Rouhani ya lashe sama da kashi hamsin da ɗaya cikin dari na ƙuri'u miliyan ashirin da biyu da aka ƙidaya ya zuwa yanzu.

Idan har Hassan Rouhani ya cigaba da samun ƙuri'un da ake ƙidayawa, to babu buƙatar zuwa zagaye na biyu a zaɓen.

Hassan Rouhani dai ya zama tamkar ɗan takarar 'yan adawa ne, inda masu hanƙoron samun sauyi a Iran suka goya masa baya.

Koda tsoffin shugabannin ƙasar Iran ɗin biyu, wato Hashimi Rafsanjani da Muhammad Khatami sun goyi bayan Hassan Rouhani.

Karin bayani