Hassan Rowhani ke kan gaba a zaben Iran

Masu aikin zabe a Iran
Image caption An fara kidayar kuri'u a iran

Sakamakon farko daga zaben shugabancin Kasar Iran ya nuna cewa Hassan Rowhani shine ke kan gaba

Sakamakon farkon sun bayyana kashi hamsin da biyu cikin dari na kuri'u miliyan biyar da aka kirga ya zuwa yanzu. Kuma Idan har ya dore akan wannan alkaluma, zai iya kaucewa tafiya zagaye na biyu na zaben

Magajin garin Tehran Mohammad Baqar shine ke biya masa

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta soma sakin alkaluman farko na sakamakon zaben ne, bayan jinkirin da aka samu na sa'oi da dama.

Shugaba Mahmud Ahmadinajad dai zai sauka ne bayan da ya kammala wa'adinsa na biyu akan mulki

Karin bayani