An yi dabar taya Sarkin Kano murna

Alhaji Ado Bayero
Image caption Ranar Asabar Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, ya cika shekaru 50 a kan gadon sarauta

A jihar Kano dake Najeriya an gudanar da wata takaitacciyar daba ko kuma jerin gwanon dawaki don taya mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, murnar cika shekaru 50 a kan gadon sarauta, da kuma cika shekaru 83 a duniya.

Fitattun 'yan Najeriya da dama ne dai suka halarci bikin wanda aka yi kofar fadar Sarkin, inda dubban mutane suka hallara.

Mai martaba Alhaji Ado Bayero dai ya hau kan gadon mukin ne ba tare da ya yi hakimci ba.