Najeriya na tangal-tangal —Nuhu Ribadu

Malam Nuhu Ribadu
Image caption Malam Nuhu Ribadu ya ce matsalolin da Najeriya ke fama da su sun kai intaha

Tsohon shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati a Najeriya, EFCC, ya ce kwatanta kasar da jirgin ruwa mai tangal-tangal.

A wata hira da ya yi da BBC, Malam Nuhu Ribadu ya ce matsololin da kasar ke fama da su, wadanda suka hada da tabarbarewar tsaro, da cin-hanci da rashawa, da kuma tauye hakkin talaka sun kai intaha.

“A yau”, inji Malam Nuhu Ribadu, “idan ka ga jinin da ake zubarwa, wani gefe na kasar nan yana cikin [dokar ta-baci], wasu wurare kuma sai tashin hankali; idan ka ga wahalar talauci, da ketare hakkin [bil-Adama], da zalunci, da kuma cin-hanci da rashawa, ina jin ba a taba samun kamar abin da ke faruwa a yanzun nan ba.

“Zan [iya cewa] kusan muna cikin wani hali—Allah Ya tsare, Ya kiyaye—wanda za a ce kasar nan tana cikin matsala sosai”.

Dan takarar shugabancin kasar a shekarar 2011 a karkashin jam’iyyar adawa ta ACN ya kuma zargi manyan kasar da gazawa wajen samar da abubuwan more rayuwa: “Ka je filin jirgin sama yanzu, tsakanin nan [Abuja] da Legas, za ka tarar da jiragen da mutane suka saya [har guda] 400 suna tsaye—ko wanne jirgi daya kuma za ka ji dalar Amurka miliyan goma, miliyan ashirin, miliyan talatin, miliyan arba’in.

“Jirgi daya zai iya gina maka [jami’a], jirgi daya zai iya gina maka asibiti babba; manya yanzu sun daina shiga jirage na haya—kowa yanzu yana [da nasa]—ba a taba samun irin haka ba”.

Malam Nuhu Ribadu ya ce dole ne gwamnatin kasar ta Najeriya ta dauki matakan magance matsalolin don hana kasar sake fadawa cikin yakin basasa.

Karin bayani