An kai munanan hare-hare a Pakistan

Gobara a wani gidan tarihi a Pakistan
Image caption Gobara a wani gidan tarihi a Pakistan

Rahotanni daga yankin kudu maso yammacin Pakistan na cewa, wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani asibiti dake garin Quetta na lardin Baluchistan.

An kuma bada rahoton fashewar wani abu a sashen kula da marasa lafiya dake bukatar kulawar gaggawa dake cikin asibitin.

A asbitin da 'yan bindiga suka kai wannan hari ne dai ake yin magani ga wasu da wani harin bam din daban ya jikkata.

Yanzu haka dai jami'an tsaro sun garzaya wurin zuwa asibitin.

Cikin 'yan watannin nan dai ana fuskantar karuwar hare-haren kungiyoyin dake dauke da makamai a yanzin na Baluchistan.

A wani labarin kuma 'yan aware dake gwagwarmaya da makamai a Pakistan din sun yi amfani da bama-bamai wajen lalata wani wuri mai muhimmanci ga tarihin kasar.

Wurin da suka lalata din dai ana kiransa, Ziyarat, wanda gida ne a yankin Baluchistan da wanda ya jagoranci gwagwarmayar kafa kasar wato Muhammad Ali Jinah yake hutu, kuma a gidan ya kasance har mutuwarsa.

Harin bam din dai ya haddasa gobarar da ta kona dukkan kayan tarihi dake cikin gidan:

Karin bayani