Turkiya: Ana ci gaba da tashin hankali

A Turkiyya ana ta ɗauki-ba-daɗi ba ƙaƙƙautawa yau tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sandan kwantar da tarzoma a birnin Santanbul bayan jami'an tsaro sun yi amfani da ƙarfi wajen fatattakar masu zanga-zanga daga dandalin Gezi cikin daren jiya.

'Yan sanda sun yi ta amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zanga.

Tuni dai aka killace wuraren ma dake kusa da dandalin na Gezi, inda ya zama matattarar masu nuna adawa da gwamnati.

Arangamar da aka yi tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga jiya a birnin Santanbul ta haifar da wata zanga-zangar a Ankara, babban birnin kasar.