Rasha ta gargadi kasashen yamma

Shugaba Putin na Rasha
Image caption Shugaba Putin na Rasha

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya ja kunnuwan kasahen yammaci game da baiwa 'yan tawayen Syria makamai.

Mr Putin na magana a nan Landan bayan tattaunawarsa da praministan Birtaniya.

A wani jirwaye mai kamar wanka da ya yi kan hoton bidiyan da ya nuna wani dan tawayen Syrian na cin naman zuciyar wani sojan gwamnati da aka kashe, Mr Putin ya ce sam bai kamata a tallafawa 'yan tawayen ba.

Mr Putin ya ce Rasha ta bi dokoki lokacin da ta samarwa gwamnatin Syria makamai, ya kuma yi kira ga kasashen da ke tunanin baiwa 'yan tawayen makamai da suma su bi ka'ida.

A na shi bangaran dai praministan Burtaniya, David Cameron cewa ya yi gwamnatin Birtaniya zata ci gaba da aiki tare da dakarun 'yan adawar Syria dake san ganin an kafa gwamnatin demokradiyya; amma dai ya kara da cewa ba'a kai ga yanke shawara kan basu makamai ba.

Karin bayani