Mace zata yi takarar shugabancin Mali

Image caption Taswirar kasar Mali

Wata 'yar majalisar dokokin Mali ta bayyana aniyarta ta tsayawa takarar shugabancin kasar da za'a yi a ƙarshen watan Yuli.

'Yar majalisar, wato Aissata Haidara Cisse, ita ce mace ta farko da zata tsaya takarar shugabancin kasar ta Mali.

Yayin da take jawabi ga wani gangami na dubban magya bayanta tace, kasar Mali tana bukatar ayukan cigaba, musamman ma tace, ya kamata a fi maida hankali ga habaka yankin arewacin kasar da 'yan tawaye suka taba kwacewa.

Mali dai ta yi fama da hare-haren 'yan tawaye masu kaifin kishin Islama da kuma kungiyoyin 'yan a ware.