Mutane na murnar nasarar Rouhani a Iran

Murnar nasarar Hassan Rowhani a Iran
Image caption Murnar nasarar Hassan Rowhani a Iran

Dubun-dubatar jama'a sun kwarara a kan titunan birnin Tehran, domin shagulgulan nasarar mai matsakaicin ra'ayin 'yan mazan jiya, Hassan Rouhani, a zaben shugaban kasar Iran.

Mista Rouhani ya bayyana sakamakon zaben a matsayin wata nasara a kan tsatstsauran ra'ayi, kuma magoya bayansa sun ce sun yi zabe ne na canji.

Mista Rouhani dai ya lashe fiye da kashi hamsin cikin dari na kuri'un da aka kada.

An dai hana 'yan takarar neman sauyi tsayawa takara a zaben.

Amurka ta ce a shirye take ta gudanar da tattaunawa ta kai-tsaye da kasar Iran game da shirinta na nukiliya, bayan zaben Mista Rouhani a matsayin sabon shugaban kasa.

Fadar White House ta yabawa Iraniyawa saboda jaruntar da suka nuna wajen ganin cewa an saurari muryoyinsu, duk kuwa da abin da ta kira matsalolin da aka samu na gwamnati da suka hada da rashin gaskiya.

Karin bayani