Matar Mandela ta ce sun gode da kulawa

Mr Mandela da Maidakinsa Graca
Image caption Mr Mandela da Maidakinsa Graca

Matar tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela, Graca Machel, ta fito a karon farko ta yi magana tun bayan kwantar bda shi a asibiti sama da mako guda kenan.

A wata rubutacciyar sanarwa da aka fitar, Graca Machel ta ce tace sakonnin fatan alheri da nuna kauna da ake ta aikawa daga sassa na duniya daban daban sun sa sun sun ji dama dama daga abi da ta kira halin fargabar da suke ciki a sakamakon ci gaba da jinyar da Nelson Mandela ke yi a asibiti.

Mrs Machel , wanda ke ci gaba da kasancewa a gefen gadon mijinta nata mai shekaru casa'in da hudu, yayinda ake masa magani kan cutar huhun da yake fama da ita, ta bayyana godiya kan abin da ta kira kauna da kuma karimcin da jama'a suka nuna ma su daga ko'ina cikin duniya.

Matar Mr Mandela ta tunatar da jama'a cewa a baya fa maigidan nata ya taba cewa, muhimmin abu a rayuwa ba wai kasancewar mun taba rayuwa ba, amma mai muka yi a lokacin rayuwar tamu domin taimaka ma wasu.

Karin bayani