Za'a gurfanar da Saif Al-Islam Gaddafi

Ofishin mai gabatar da kara a Libiya ya sanar cewa, a watan Agusta mai zuwa, dan tsohon shugaban kasar, Sayef Al-Islam Gaddafi, da wasu manyan jami'an gwamnatin Gaddafi za su gurfana a gaban kotu.

Za a tuhume su da aikata wasu munanan laifufuka a lokacin juyin juya halin shekara ta 2011, lokacin da aka kawar da jagoran kasar, Muammar Gaddafi.

Baya ga dan marigayi Gaddafi, wadanda za su gurfana a gaban kotun sun hada da tsohon shugaban hukumar leken asiri ta soji, Abdullah Sunusi, da kuma wasu jami'ai da dama.

A halin da ake ciki kuma wata kotu a Libiyar ta yanke hukunci na farko na wasu kararraki da aka shigar gabanta, akan wasu tsoffin shugabannin gwamnatin Gaddafi.

Kotun ta birnin Tripoli ta wanke tsohon ministan harkokin waje ,Abdelaaty al Obeidi, da kuma Mohammed Al-Zway, shugaban majalisar kasa ta Libiyar.

An zargi mutanen biyu ne da yin wadaka da dukiyar kasa, ta hanyar amincewa da biyan diyya ga wadanda harin jirgin Lockerbie na shekarar 1998 ya ritsa da su.

Sai dai kuma za'a cigaba da tsare mutanen biyu, domin fuskantar wata shari'ar a cikin watan Augusta.