Valerie Amos ta ziyarci jihar Kogi

Ambaliyar ruwa a nijeriya
Image caption Ambaliyar ruwa a nijeriya

Babbar Jami'ar bada agajin gaggawa, karkashin ofishin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Valerie Amos ta kai ziyarar aiki na kwanaki biyu Najeriya.

A lokacin ziyar tata dai ta je wasu Jihohi da ambaliyar ruwa ta shafa a bara, ciki har da jihar Kogi.

Mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa sun bayyana cewa suna cikin wani mawuyacin hali.

Hukumar kula da hasashen yanayi a kasar ta yi hasashe cewa, akwai yiwuwar a sake yin ambaliyar ruwa a wasu sassa na kasar a bana.

A bara dai miliyoyin mutane ne suka rasa gidanjensu da gonakinsu, yayin da a wasu yankunan ma suka yi asarar dabbobi.

Lamarin da kuma yayi sanadiyyar rasa rayukan kusan mutane 300.