Kungiyar gwamnonin Najeriya ta rabu

A Najeriya barakar da ta kunno kai game da shugabancin kungiyar gwamnonin kasar na dada karuwa.

Bangaren gwamna Jonah Jang ya kira taron gwamnonin a yau, domin tattauna wasu muhimman batutuwa.

To amma bangaren gwamna Rotimi Amaechi ya ce shi bai san da wani taro ba.

A wani labarin kuma in an jima ne shugaba Goodluck Jonathan zai shirin ganawa da gwamnonin kasar su talatin da shidda.

Rabon arzikin kasar na daga cikin manyan batutuwan da ake sa ran za su tattauna a kai.

A makon da ya wuce wata dambarwa ta barke game da rabon kudaden, tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi.