''Iran za ta kyautata hulda da kasashen duniya''

Sabon shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani, ya ce a yanzu kasarsa ta sami sabon zarafi na kyautata hulda da sauran manyan kasashen duniya.

Ya bayyana hakan ne a ganawarsa ta farko da manema labarai, tun bayan da ya lashe zaben da aka gudanar a ranar Juma'a.

Musamman shugaba Rouhani ya jinjina wa matasan kasar, kan yadda suka guji nuna halayya irin ta masu tsatsauran ra'ayi.

Sabon Shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce yana fatan duniya za ta samu damar yin mu'amala ta kwarai tare da Iran.

Ya ce dangantaka tsakanin Iran da Amurka wani tsohon miki ne da ake bukatar magancewa.

Sai dai bai ce wani abu sabo ba, a kan shirin nukiliyar Iran da ake takaddama a kansa.

A yau an ambaci shugaban hukumar sa ido kan makamashin nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya, IAEA, Yukiya Amano na cewa akwai alamun Iran din na ci gaba da shirin nukiliyarta, duk kuwa da takunkumin da wasu kasashen duniya suka saka ma ta.

Karin bayani