An kashe dalibai tara a Maiduguri

Maiduguri
Image caption Wasu dalibai a Maiduguri

Wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan kungiyar nan ce ta Jama'atu AhlisSunna Liddawati wal jihad, da aka fi sani da Boko Haram sun bude wuta kan wasu dalibai dake rubuta jarrabawa a wata makaranta, a birnin Maiduguri dake jihar Borno a Najeriya.

Harin dai yayi sanadiyyar mutuwar akalla daliban makarantar tara.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun kaddamar da hare-haren ne a wata makaranta mai zaman kanta, mai suna Ansarudeen a ranar Talatar da ta gabata.

Wani jami'i dake aiki a wani asibiti a Maiduguri, wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya shaida wa manema labarai cewa an kawo gawawwakin daliban asibitin, wadanda dukkaninsu ke sanye da kayan makaranta a jikinsu.

Harin na zuwa ne 'yan kwanaki bayan wasu 'yan bindiga sun kashe wasu dalibai bakwai tare da malamansu biyu, a wata makarantar sakandare dake garin Damaturu na jihar Yobe.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba