Taliban sun kashe sojojin Amurka a Bagram

Afghanistan
Image caption Sansanin sojin sama na Amurka a Bagram

An hallaka wasu sojojin Amurka hudu a sansanin sojin saman Bagram dake Afghanistan, a ranar da Amurka ta sanar da cewa za ta fara tattaunawa da 'yan kungiyar Taliban.

A wani sakon wasikar intanet ta E-mail da Taliban ta aike wa BBC ta ce, ita ke da alhakin kai harin.

'Yan jarida masu aika rahotanni sun ce harin na nuna irin matsalolin da ka iya kawo cikas ga tattaunawar, wadda ake sa ran farawa ranar Alhamis a Qatar.

Dama dai Shugaba Obama ya ce shirin tattaunawar, ba zai kasance cikin sauki ko hanzari ba.

Kuma ya jaddada cewa ba za a dakatar da aikin sojin Amurka na fafata yaki ba, duk da fara tattaunawar da kuma mika ikon kai hare-haren ga jami'an tsaron Afghanistan.