Mutane na boren karin kudin mota a Brazil

masu zanga zanga a Brazil
Image caption masu zanga zanga a Brazil

A Brazil mutane fiye da dubu dari ne suka bazama kan tituna domin gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin kudin shiga motocin haya domin karbar bakuncin gasar cin kwallon kafa na duniya a shekara ta 2014.

An gudanar da zanga-zangar mafi girma a Sao Paolo da kuma Rio de Janaeiro.

Rahotanni sun ce zanga-zangar itace mafi girma a kasar, cikin fiye da shekaru ashirin

An soma zanga-zangar ne a makon da ya gabata, bayan da aka bayar da sanarwar kara kudin motar safa.

A babban birnin Kasar na Brasilia, masu zanga-zangar sun keta shingen tsaro a majalisar dokokin kasar, inda suka haye kan rufin ginin majalisar.

Karin bayani