Fashin teku: Yammacin Afrika ya fi Somalia

Fashin teku na karuwa a gabar tekun yammacin Afrika
Image caption Duk da cewa an fi samun fashin teku a yammacin Afrika, yankin baya samun sa ido kamar Somalia

Yawan fashin tekun da ake samu a gabar tekun yammacin Afrika ya zarta wanda ake samu a Somalia, a cewar wani rahoto na hukumar sa ido kan zirga-zirgan jiragen ruwa ta kasa da kasa.

Hakan na kunshe ne a wani rahoto da hukumar sa ido a kan sufurin jiragen ruwa na kasa da kasa tare da wasu kungiyoyi suka fitar.

Rahoton yace an cafke ma'aikatan jiragen ruwa 966, a gabar tekun yammacin Afrika a shekarar 2012, idan aka kwatanta da mutane 851 da aka kama a gabar tekun Somalia.

Masu fashin teku a yammacin Afrika a yawancin lokuta na satar man jiragen da kuma kayayyakin ma'aikatan jiragen, sannan ta kan kai su da yin amfani da karfi.

An kashe biyar daga cikin mutane 206 da aka yi garkuwa da su a bara, a cewar rahoton.