Mali ta cinma sulhu da Azbinawa 'Yan tawaye

Wakilan Azbinawa 'yan tawaye na Mali
Image caption Wakilan Azbinawa 'yan tawaye na Mali

A karshe dai gwamnati a kasar Mali ta sa hannu a kan wata yarjejeniya tare da 'Yan tawayen awaren Azbinawa domin karbar iko da babban gari na karshe da suke iko da shi a arewacin kasar, Kidal.

An cimma yarjejeniyar ne bayan tattaunawar kwanaki goma a Burkina Faso mai makwabtaka da su.

A karkashin yarjejeniyar, dakarun Mali za su sake karbar iko da Kidal gabanin zaben shugaban kasar da za a yi cikin wata mai zuwa.

A bara ne 'yan kishin Islama tare da kawancen Azbinawa 'yan aware suka kwace iko da fiye da rabin kasar Mali, kafin Faransa da hadin gwiraw dakarun kasashen Afrika ta yamma su fatattake su.