Sojin Afghanistan sun karbi iko da tsaro

Dakarun sojin Afghanistan
Image caption Dakarun sojin Afghanistan

Dakarun Afghanistan sun karbi ragamar kula da tsaron a fadin kasar, a karo na farko tun bayan da dakarun Nato suka kifar da gwamnatin Taliban a shekarar 2001.

A wani biki da aka yi a birnin Kabul, shugaba Hamid Karzai ya ce "Daga ranar Laraba dakarunmu ne za su jagoranci dukkan al'amuran tsaro."

Masu sharhi sun ce kwararru cikin sojojin Afghanistan za su iya tunkarar batun tsaro, sai dai akwai dan tababa game da wadanda basu kware ba.

Dakarun kasashen waje za su cigaba da kasancewa a Afghanistan har zuwa karshen shekarar 2014.

Inda za su dinga agazawa dakarun Afghanista, inda ake bukatar hakan.

Karin bayani