Obama zai gana da Angela Merkel

Obama
Image caption Shugaba Obama da takwarorinsa a taron G8

Nan gaba a yau Laraba ne shugaban Amurka Barack Obama zai gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a Berlin, bayan halartar taron manyan kasashe 8 masu karfin tattalin arziki a Arewacin Ireland.

Ana sa ran shugaban zai gabatar da jawabi na neman aiwatar da manyan bukatun wannan karni , a wurin kofar nan mai tarihi ta Brandenburg, wato ta tsohon Bangon Berlin da ke babban birnin Jamus.

Jami'ai sun ce a jawabin nasa zai bukaci kasashen yammacin duniya su hada kai domin fuskantar manyan kalubalan karni na 21 , da suka hada da sauyin yanayi da bazuwar makaman kare dangi.

Shekaru biyar da suka gabata ne Mr Obama, ya ziyarci birnin na Berlin a lokacin yana matsayin dan takarar shugabancin Amurka inda yayi jawabi ga taron jama'a da ke cike da annashuwa ta jin dadin kalamansa game da kura-kuran Amurka.