Amurka na shirin ganawa da Taliban

Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce Amurka za ta soma tattaunawar kai-tsaye tare da Taliban a cikin 'yan kwanaki masu zuwa.

Za'a yi taron ne a kasar Qatar, inda ake sa ran 'yan tawayen Afghanistan za su bude ofishinsu na farko a kasar waje wanda aka jima ana jiran su yi.

Tunda farko Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan ya ce gwamnatinsa ma za ta aika da wata babbar tawaga zuwa Qatar domin tattaunawa da 'yan Taliban din.

Ya ce: "Muna fatar cewar 'yan Taliban, yan uwammu, za su fahimci haka suma, cewar ya kamata a maido da wannan yunkuri zuwa kan doron kasarsu, kasar kanmu, Afghanistan, kuma dole a tabbatar da zaman lafiya".

To amma a kodayaushe 'yan Taliban na kin ganawa da Shugaba Karzai ko gwamnatinsa, suna masu yin watsi da shi a matsayin dan koren Amurka.

Karin bayani