Mutane 11 sun mutu a harin Damaturu

Rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta JTF na rangadi
Image caption Rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta JTF na rangadi a birnin Maiduguri, makociyar jihar Yobe

A Najeriya, hukumomin soji sun ce akalla mutane 11 ne suka mutu, a wani hari da ake zargin 'yan kungiyar Jama'atul AhlusSunna Lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram sun kai a jihar Yobe.

Maharan sun kashe mutanen ne a wata makaranta a Damaturu, babban birnin jihar.

Rundunar tsaro ta JTF a jihar ta bayyana cewa ta yi nasarar cafke wasu 'yan kungiyar su uku.

Hakan ya faru ne a wani artabu da sojojin suka yi da 'ya'yan kungiyar a wani wajen duba ababen hawa a garin.

Gwamnatin jihar Yoben dai ta yi tur da hare-haren, inda ta bukaci al'ummomin jihar su cigaba da ba da hadin-kai ga jami'an tsaro, domin magance matsalolin tsaron da ake fuskanta.

Hakan na faruwa ne a lokacin da jihar tare da makociyarta ta Borno da kuma Adamawa ke cigaba da kasancewa cikin dokar ta baci da gwamnatin Najeriyar ta sanya musu.