An kashe mutane sama da 40 a Zamfara

Jami'an tsaron Nijeriya
Image caption Jami'an tsaron Nijeriya

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya na cewa, fiye da mutane arba'in ne aka kashe a garin Kizara da ke Karamar Hukumar Tsafe da ke Jihar ta Zamfara.

Hukumomi sun ce, wasu mutane dauke da makamai da ake sa ran 'yan fashi ne, su ne suka kai wannan hari.

Bayanai sun nuna cewa, daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da Basarake, da kuma babban limamin garin.

Kakakin gwamnatin jihar ta Zamfara ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar ta Zamfara na daga cikin wasu manyan jami'ai da suka ziyarci garin domin ganin irin abubuwan da suka auku.

Mazauna yankin sun ce harin yana kama da na ramuwar gayya.

Kauyuka a jihar ta Zamfara da wasu yankuna masu makwabtaka da su na fama da irin wadannan hare hare da ake dangantawa da wasu 'yan fashi dake cewar suna daukar fansar kisan wasu 'yan uwansu da aka kashe.