Afghanistan ba zata yi sulhu da Taliban ba

Hamid Karzai

Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai ya ce gwamnatinsa ba zata bi sahun shawarwarin neman sulhu tare da kungiyar Taliban ba, har sai idan Afghanistan ce zata jagoranci shirin.

Ranar Alhamis ne aka shirya, Amurka zata fara tattaunawa da kungiyar Taliban a Qatar, inda kungiyar ta bude ofishinta.

Mr Karzai ya ce bude ofishin ya sabawa tabbascin da gwamnatin Amurka ta baiwa gwamnatinsa a baya, don haka ya jingine duk wasu shawarwari na neman wanzar da zaman lafiya tare da Amurka don nuna rashin amincewarsa.

Shugaba Obama ya ce da ma Amurka ta yi zaton samun sabani tsakaninta da gwamnatin Afghanistan, to amma yace yayi imani yana da matukar muhimmanci a rungumi yiwuwar samun sasintawa da masu tsaurin ra'ayin da hannu bi-biyu.