Mali ta cimma yarjejeniyar da 'yan tawaye

'Yan tawayen Azbinawa
Image caption Babbar kungiyar 'yan tawayen ta MNLA data hannu a yarjejeniyar ta kulla kawance da kungiyar AlQaida

Gwamnatin Mali ta sanya hannu a yarjejeniya tare da 'yan tawayen Azinawa, wacce zata kai ga yin zabe a watan gobe.

A karkashin yarjejeniyar dai za a tsagaita wuta nan take, kuma dakarun gwamnati za su koma garin Kidal da 'yan tawaye ke da karfin iko, a cewar jami'ai.

'Yan tawayen dai sun karbe iko da garin na Kidal ne bayan dakarun da Faransa ke jagoranta sun fatattaki masu fafutukar Islama daga garin a watan Fabrairu.

Azbinawan na fafutukar samun cin gashin kan arewacin kasar, tun bayan lokacin da Mali ta samu 'yancin kanta daga Faransa a shekarar 1960.

Suna korafin cewa gwamnatin kasar dake da fada a Bamako babban birnin kasar na nuna musu wariya.

A lokacin da yake sanar da cimma yarjejeniyar, bayan kammala taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G8 a Ireland ta Arewa, shugaban kasar Faransa, Francios Hollande ya ce yarjejeniyar za ta kaiga samun yin zaben shugaban kasa a fadin Mali har da garin Kidal.