Cikas a yunkurin sulhu da Taliban

Ofishin Taliban a Qatar
Image caption Ofishin Taliban a Qatar

Yunkurin da ake yi na fara tattaunawar zaman lafiya kan Afghanistan a Qatar, na cigaba da fuskantar cikas saboda takaddamar da ake yi game da matsayin sabon Ofishin 'yan Taliban da aka bude a kasar.

Bayan da hukumomin Qatar suka ja kunnen su, 'yan kungiyar Taliban din sun cire tutarsu da wata alama da ke cewa daular Islama ta Afghanistan a ofishin.

To saidai daga bisani sun sake maida wadannan alamu a kan wani gajeren tirke na kafa tuta.

A wata hira da BBC, wani wakilin gwamnatin Afghanistan ya yi watsi da nacewar da 'yan Taliban suka yi cewa ofishin nasu dake Doha, zai kasance ne a matsayin wani ofishin jakadanci, ba kawai wurin da za a yi tattaunawar zaman lafiyar ba.