Brazil na kokarin shawo kan masu zanga-zanga

Wutar artabun da aka yi a Brazil
Image caption Wata wutar da masu zanga-zanga suka kunna a Brazil

Shugabar kasar Brazil Dilma Roussef ta yi alkawarin duba bukatun masu zanga- zanga bayan tarzomar da aka shafe sama da mako daya ana yi a fadin kasar.

A wani jawabi da ta gabatar ga al'ummar kasar Madam Roussef ta ce zata inganta harkar sufurin gwamnati da ta kula da lafiya da kuma ilimi.

Haka kuma ta kare yawan makudan kudaden da ake kashewa a kan shirye shiryen gasar wasan cin kofin duniya ta kwallon kafa da za a yi a kasar a badi, inda ta ce ba wai ana kashe wadannan kudaden ba ne a maimakon zuba su a ayyukan kula da jin dadin jama'a.

Shugabar ta yi alkawarin ganawa da masu zanga- zangar ta lumana.

Sai dai masu zanga-zangar sun musanta rahotannin da ke cewa sun amince su dakatar da boren - inda suka ce za su ci gaba da gwagwarmaya.

Karin bayani