Brazil ta shiga rudani

Zanga-zanga a Brazil
Image caption Zanga-zanga a Brazil

An tsaurara matakan tsaro a manyan biranen Brazil, gabannin jerin zanga-zangar da aka shirya yi a kan batutuwa da dama.

Masu zanga zangar na kokawa da rashin ingancin hanyoyin sufuri da matsalar cin hanci da rashawa da kuma yawan kudaden da za a kashe a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da za a yi badi a kasar.

Yanzu haka dai hukumomi sun sa katako sun rufe kofofin shiga tashoshin jiragen kasa da shaguna da kuma gine-ginen gwamnati a biranen Sao Paulo da Rio de Janeiro.

An shirya za a yi jerin zanga-zangar ne a birane fiye da 80 na kasar ta Brazil.

Karin da aka yi har zuwa kashi 10 daga cikin 100 na kudin sufuri a farkon wannan watan shine ya haddasa jerin zanga-zangar.

An soke karin a jiya, amma jama'a sun cigaba da zanga-zangar.

Karin bayani