Kotu ta sami 'yan Kabilar Uighurs da laifi

China Uighurs
Image caption Wani masalaci na kabilar Uighurs a yankin Xinjiang

Hukumomin China sun yanke wa wasu mutane 11 hukuncin zaman gidan yari na zuwa shekaru 6 akan laifukan addini da kabilanci a yankin yammacin kasar na Xinjiang.

Wa'adi mafi tsawo da aka yanke wa wani daga cikin mutanen shi ne na laifin amfani da intanet wajen kira da ayi jihadin musulunci.

Sauran mutanen an zarge su ne da laifin shiga gidajen mutane da karfin tsiya suka farfasa talabijin a rikicin addini.

Dukkanin mutanen dai ana ganin 'yan kabilar Uighurs ne wadanda musulmi ne marassa rinjaye .

An yanke wannan hukunci ne jim kadan kafin zagayowar shekara hudu da lokacin da aka yi gagarumin rikicin kabilanci na adawa da kabilar sinawa wanda hukumomi suka murkushe da karfi.

China ta dora alhakin tashe- tashen hankulan a kan kungiyar 'yan ware ta kabilar Uighurs sai dai al'ummar musulmin dake da rinjaye a yankin Xinjiang sun koka kan yadda ake takurawa adininsu da al'adunsu.