'An kama maharan da suka kashe dalibai'

Maiduguri
Image caption Wasu sojojin Najeriya dake sintiri a birnin Maiduguri

Shalkwatar tsaro ta Najeriya ta ce sojoji sun kama wasu mutane 8 da ake zargin 'yan kungiyar nan da ake kira Boko haram da suka kai wa wasu makarantun sakandare biyu hari a jihohin Borno da Yobe.

Kakakin Shalkwatar tsaron Brigedier Janar Chris Olukolade ya shaida wa BBC cewa an kama maharan ne, a wajen garin Maiduguri kuma sojoji sun kashe biyu daga cikinsu.

Sai dai ya ce hare- haren baya bayanan da ake zargin 'yan kungiyar da kaiwa makarantu, wata dabara ce ta sanya tsoro a zukatun jama'a da kuma nuna cewa har yanzu suna nan da karfi duk da yadda jamian tsaro suka karya lagonsu.

A ranar lahadin din data gabata ne wasu 'yan bidiga suka bude wuta a wata makarantar sakadare a jihar Yobe inda suka kashe dalibai bakwai da kuma malamansu biyu.

Ha kama a Maiduguri 'yan bindigar sun kashe dalibai tara a wata makarantar sakadare, a lokacin da suke rubata jarabawa ranar litinin din data gabata.

Sai dai kamen da hukumomin tsaro ke ikirarin yi na zuwa ne, bayan da aka haramta amfani da wayar tauraron dan Adam ta Thuraya a jihar Borno .

Hukumomin tsaron dai na zargin an yi amfani da wayar Thuraya wajen tsara kai harin.