Mutane uku sun hallaka a Canada

Akalla mutane uku ne suka rasu kuma wasu dubbai suka tsere daga gidajensu a yammacinkasar Canada a dalilin ruwan sama mai karfi da ya haddasa ambaliya.

Hukumomin kasar sun bukaci a kwashe mutane daga yankin tsakiyar birnin Calgary bayan da kogunan birni biyu suka tumbatsa suka yi ambaliya.

Ambaliyar ta rushe gadoji da tituna, ta tsinke wayoyin lantarki ta kuma mamaye gidaje

Hukumomin na kuma shirin kwashe dabobbi daga gidan dabbobi na Calgary.