Pakistan: An kashe mutane 15

Image caption An yawan kai hare-haren bam dake hallaka jama'a a Pakistan

'Yan sanda a Pakistan sun ce masu fafutikar Islama sun kashe mutane goma sha biyar a wani hari da suka kai wa wani masallacin 'yan Shi'a da wata makarantar Islama dake birnin Peshawar na Arewa maso yammacin ƙasar.

Da farko masu fafitukar sun buɗe wuta ne a kan ɗaruruwan masu ibada dake halartar Sallar juma'a, daga bisani kuma, wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tada nakiyoyin dake jikinsa.

Wasu karin jamaa da dama sun samu raunika.

Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma a 'yan shekarun nan, an samu karuwar hare-haren da ake kaiwa a kan 'yan Shia, wadanda 'yan tsiraru ne a kasar ta Pakistan.