Amurka ta shigar da kara a kan tsohon jami'in leken asirinta

Amurka Snowden
Image caption Wasu magoya bayan Mr Edward Snowden a Hongkong

Amurka ta shigar da karar aikata manyan laifuka akan tsohon jami'in leken asirinta da ya fallasa shirinta na satar jin bayanai da sadarwar intanet na jama'a.

Tsohon jami'in asirin na Amurka Edward Snowden na fuskantar tuhuma ne ta leken asiri da sata.

Haka kuma rahotanni sun ce Amurkan ta bukaci hukumomin Hong Kong su tsare mata shi ko da ike babu tabbacin cewa yana Hong Kog din har yanzu.

Mr Snowden ya tsere ne zuwa Hong Kong ne bayan ya fallasa shirin hukumomin asiri na Amurkan na tattara bayanai kan sadarwar miliyoyin jama'a ta intanet da ta wayar tarho.