Karuwar mutuwar Mata wajen haihuwa a Nijer

Mata masu juna biyu a Nijer
Image caption Mata masu juna biyu a Nijer

A Jamhuriyar Nijar, wani batu dake cigaba da ciwa mahukunta tuwo a kwarya shine na yawan mutuwar mata a yayin haihuwa, lamarin da yasa ake ganin da wuya kasar ta cimma muradin karni na majalisar dinkin duniya a shekarar 2015.

A yayinda ake cikin wannan damuwa,a jihar Maradi, matan dake zuwa asibiti haihuwa, sun zargi likitoci da yi musu tiyata don cire musu 'ya'ya koda kuwa za su iya haihuwa, suna masu cewa hakan na faruwa saboda rashin hakurin likitocin, duk da yake dai likitocin sun karyata wannan zargi.

Karin bayani