Ƙishi ya kashe wasu magidanta a Saudiyya

Saudi deaths
Image caption Wannan labarin ya tayar da hankalin jama'a sosai

Wani mutum da mai dakinsa sun rasa rayukansu sakamakon ƙishin da suka yi fama da shi bayan da suka bata a yankin hamadar sahara a kasar Saudi Arabia.

Hukumomin tsaro na kasar ta Saudiyya sun kaddamar da gagarumin aikin ceto domin nemo ma'auratan biyu - wadanda yan kasar Qatar ne.

Daya daga cikin 'yan uwansu ne ya sanar da jami'an tsaro cewa sun bata.

Wannan ba karamin mummunan labari bane ga hukumomi a kasar ta Saudiyya.

An gano gawar matar ne kusa da motar da suke tafiya a ciki wacce ta hantsila.

Daga bisani kuma wani jirgin helkwabta na jami'an agaji ya gano gawar mijinta kusan tazarar kilomita goma tsakaninsu.

Alamu sun nuna cewa ya yi kokarin samo ruwan sha ne - ko kuma kai mata dauki - a cikin saharar mai girman gaske.

Yayin da yanayin zafi ke kara tsananta sosai, saharar wani yanki ne mai illar gaske ga dan adam.

Wuri ne da babu ruwa kuma ana yi masa kallon inda bil'adama ba zai iya zama ba - in banda wani dan wuri da akan yi amfani da shi lokaci-zuw alokaci.

Karin bayani