Snowden zai kwana a Moscow

Edward Snowden, tsohon jami'in da ke kula da bayanan sirrin tsaro Amurka zai kwana a filin saukar jiragen saman Moscow, babban birnin kasar Rasha, kuma daga nan gobe ya zarge zuwa Cuba.

Kuma rahotanni na cewa, hukumomin Amurka sun soke fasgo ɗin Snowden.

Hukumomin yankin sun ce, Edward Snowden, ya fice daga Hong Kong ne bisa raɗin kansa bayan ya fallasa wani shirin tattara bayanan sirri ta hanyar sadarwa ta intanet da Amurka take gudanarwa a China.

Hakika wannan zai zama wani gagarumin koma baya ga Amurka wacce tuni ta soma daukar matakan tusa keyarsa zuwa gida.

Ranar Asabar fadar gwamnatin Amurka ta White House ta tuntubi Hong Kong da nufin shirya yadda za a mika mata Mista Snowden, amma yanzu hukumomin yankin sun ce takardun da Amurka ta gabatar ba su cika ka'idojin da aka tanada a karkaahin dokokin Hong Kong ba.

Karin bayani