'Yan tawayen Syria za su samu karin tallafi

Yan tawayen Syria
Image caption Yan tawayen Syria sun ce suna bukatar taimakon manyan makamai

Ministocin harkokin waje na kasashen da suke kiran kansu kawayen Syria, sun amince su bayar da taimakon gaggawa ga 'yan tawayen kasar ta Syria.

A wani taro da suka gudanar a kasar Qatar, sun amince su tallafawa 'yan adawar Syria da dukkan kayayyaki da makaman da suka kamata domin su shawo kan hare-haren da dakarun gwamnati da masu mara musu baya suke kai musu.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya jaddada cewa ta hanyar siyasa ce kawai za a iya shawo kan rikicin ba wai karfin soji ba, sai dai bai ambaci wata hanya ta yin hakan ba.

Fira ministan Qatar Sheikh Hamad bin Jassim al-Thani ya ce mai yiwuwa samar da makamai ga 'yan tawayen ita ce hanya daya tilo da za a samar da zaman lafiya a Syria.

Iran da Hizboullah

Hadin gwiwar kasashen sun kuma yi Allah wdaai da gwamnatin Bashar Al Asad, kan yadda take amfani da mayaka daga kasar Iran da kuma kungiyar Hezboullah.

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya yi kira ga kasar Iran da kungiyar 'yan Shi'a ta Hezboullah, da su daina shiga cikin rikicin na Syria, inda ya yi tsokaci kan irin rawar da Hezboullah ta taka wurin sake kwace garin Qusair.

Kungiyar kasashen da ke kiran kansu kawayen na Syria, sun hada da Amurka da Burtaniya da Faransa da Jamus, da ma Saudi Arabia da Turkiyya, da Qatar da Jordan da kuma Masar.

Kimanin mutane 90,000 ne aka kashe tun bayan fara rikicin wanda aka shafe shekaru biyu ana yi a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Karin bayani