Amurka na matsawa Hongkong akan Edward Snowden

Edward Snowden
Image caption An zargi Edward Snowden ta fallasa asirin Amurka

Amurka na matsawa hukumomin Hongkong lamba domin ta mika mata Edward Snowden, tsohon jami'in leken asirin da ake zargi da fallasa asirin aikin sa'idon gwamnatin Amurka.

Wani babban jami'in Amurka ya gargadi Hong Kong da cewa duk wani jan kafa da ta yi na bada hadin kai, ka iya gurgunta dangantakar su.

Ba a kaiga sanin ko Kasar China zata tsoma bakinta cikin shirin tusa keyar tasa ba.

Mr. Snowden dai ya tsere zuwa Amurka ne a watan daya gabata, kuma Hongkong nada yarjejeniyar tusa- keyar mutane tare da Amurka.

Tuni dai 'yan Kasar ta Hongkong din suka soma bayyana ra'ayoyinsu game da batun tusa keyar sa.

Karin bayani