Masar: Soja sun yi jan kunne

Soja suna da tasiri a siyasar Masar
Bayanan hoto,

Soja suna da tasiri a siyasar Masar

Rundunar sojan Masar tayi kashedin cewa, ba zata ta bari kyasar ta auka cikin wani mummunan rikici ba.

Sojan sun yi wannan jan kunne ne gabanin zanga-zangar nuna adawa da shugaba Muhammad Morsi da za'a gudanar a karshen makon gobe.

Babban kwamandan dakarun kasar yace, idan aka yi kokarin kalubalantar zabin jama'a soja ba zasu tsaya kawai suna kallo ba.

Wannan dai shi ne tsoma baki cikin sha'anin siyasar Masar mafi girma tun bayan soja sun mika mulki ga shugaba Muhammad Mursi shekara guda da ta gabata.