Takaddama da kamfanin Shivam a Nijar

Tutar Nijar
Image caption Tutar Nijar

A jamhuriyar Nijar, wata kungiyar 'yan kasuwa masu shigowa da fitar da kayayaki zuwa kasashen waje, ta ce za ta kai karar kamfanin Shivam na kasar Indiya da ke da cibiyarsa a Yamai.

Kungiyar, wadda Alhaji Sani Shekarau Garo ke jagoranta, ta ce kamfanin Shivam ba shi da hurumin hana 'yan kasuwar Nijar shigo da kayayaki kirar Sharp a cikin kasar.

Kamfanin na Shivam ya ce shi kadai ke da izinin sayar da ire iren wadannan kayayaki a kasar ta Nijar.

Wannan ce kungiyar 'yan kasuwa ta biyu a Nijar din da ke kai karar kamfanin Shivam a kotu dangane da wannan batu.