Saudiyya ta canza ranakun hutun ƙarshen mako

Image caption Sarki Abdallah na Saudiyya

Hukumomin Saudiyya zasu canza ranakun hutun ƙarshen mako inda za'a koma yin hutun ƙarshen makon daga ranakun Juma'a zuwa Asabar.

Sadiyyar ta ɗau wannan mataki ne domin daidaita tsarin hutun karshen makon ya dace da na sauran kasashen dake yankin.

Sarki Abdallah ne dai ya fitar dokar yin wannan canji da zai soma aiki daga ƙarshen makon dake tafe.

Dama a yankin Gulf Saudiyya ce kaɗai ƙasar da ta ke yin amfani da tsarin ranakun aiki da suka soma daga Asabar zuwa Laraba.

Sarki Abdallah yace, anyi wannan canji ne domin ya zama dole domin irin damar da zai samar ta fuskar tattalin arziƙi.

Koda ƙasar Oman ma tayi irin wannan canji a watan da ya gabata.